
Limamin Kirista, Most Rev. Matthew Kukah ya bayyana cewa rahoton yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi ba gaskiya bane.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya halarta a Kaduna.
Yace niyyar kashe-kashen da ake yi a Najeriya ba na Khisan Kyiyashi bane.
Yace ko da yawan coci-coci da aka ce ana konawa duk shekara shima karyane bai san inda aka samu wadancan bayanai ba.
Bishop Kuka a baya ya sha suka a tsakanin Kiristoci bayan da yace kada a saka Najeriya cikin kasashen da akewa Kiristoci Khisan Kyiyashi.