
Malamin Kirista, Matthew Hassan Kuka ya bayyana cewa, kaso 80 na masu ilimin Najeriya Kiristoci ne hakanan kuma Kiristoci ne ke juya kaso 85 na tattalin arzikin Najeriya.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro a Kaduna inda yace to a hakane za’a ce ana yiwa Kiristoci wariya ko ana hanasu yin addinin su ko ana musu Khisan Kyiyashi a kasarnan?
Yace maganar Khisan Kyiyashi da ake cewa anawa Kiristoci a Najeriya ba gaskiya bane.
Yace ba a gane kisan Kiyashi ta hanyar yawan mutanen da aka kashe, ana ganewa ne ta hanyar niyyar me yin Khisan.