
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, shugaban kasar Amurkar Donald Trump ya baiwa shugaban kasar Venezuela, Maduro Umarnin ya sauka daga shugabancin kasar ko ya dandana kudarsa.
Rahotanni sun ce shugaba Trump na ikirarin yakar ayyukan masu safarar miyagun kwayoyi ne amma kuma wasu na zargin cewa, Trump na kokarin satar man fetur din kasar Venezuela ne.
Hakan na zuwane bayan da Bidiyo ya bayyana ind aka ji Trump na bayyana son samun man fetur daga kasar Venezuela kyauta.
Tuni dai rahotanni suka ce Amurka ta jibge jiragen ruwan yaki da dakarun sojoji a ruwan dake kusa da kasar ta Venezuela.