
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka ce ta matsawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Lamba akan ya sauke Ministan tsaro, Muhammad Badaru kamin ta amince ta hada kai da Najeriya wajan magance matsalar tsaron.
Rahotan yace Gwamnatin Amurka ta baiwa Najeriya Sharadin sai an sauke Badaru da Matawalle a matsayin Ministocin tsaro kamin ta yadda ta yi aiki da Najeriya.
Yanzu haka an ce Shugaba Tinubu na shan matsin lamba da ya sauke Matawalle daga mukamin karamin Ministan tsaro.
Tuni dai shi Muhammad Badaru ya sauka daga mukamin da kansa inda yace bashi da lafiya ne.
Hakanan rahotanni sun ce shugaba Tinubu ya gayawa tsohon shugaban sojoji, Janar Christopher Musa cewa shine sabon Ministan tsaron.