Wednesday, April 8
Shadow

Da Duminsa: Kalli Bidiyon yanda Dambarwa ta barke a majalisa inda wasu sanatoci suka ce a bar Janar Christopher Musa ya wuce amma wasu sukace basu yadda ba sai an masa tambayoyin da suka kamata

An samu dambarwa a majalisar Dattijai yayin tantance janar Christopher Musa a matsayin Ministan tsaro.

Sanata Sani Musa daga jihar Naija ya nemi a bar Janar Christopher Musa ya wuce kamar yanda aka sabawa ministocin da aka aika majalisar dan a tantancesu.

Yace Janar Musa tsohon sojane sannan kuma duk tambayoyin da suke masa yanzu sun taba masa irinsu a baya dan haka shi a shawarce yana ganin a kyaleshi ya wuce kawai.

Saidai bai samu goyon bayan sauran ‘yan majalisar ba inda suka ce ya kamata a tsaya a masa tambayoyin da suka kamata.

Karanta Wannan  An kama tsaffin shuwagabannin kamfanin man Fetur na kasa da aka sauke satin da ya gabata bisa zargin sun sace kudaden da aka ware dan gyaran matatun man Najeriya, An gano Naira Biliyan 80 a Asusun daya daga cikinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *