Friday, December 5
Shadow

Peter Obi yayi Allah wadai da rabon motocin yakin neman zaben Tinubu na 2027 yayin da Talakawa ke cikin matsi

Ba Daidai Ba Ne Raba Motocin Kamfen Yayin Da Talakawa Ke Fama Da Yunwa, Obi Ya Soki Gwamnatin Tinubu

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya soki raba motocin alfarma ga wakilan ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors domin shirye-shiryen zaɓen 2027, lamarin da ya danganta ga gwamnatin Tinubu.

A sanarwar da ya fitar, Obi ya ce wannan aiki tsananin rashin tausayi ne da cin amana, musamman a lokacin da ƴan ƙasa ke fama da yunwa, rashin aikin yi da matsalolin tsaro.

Ya jaddada cewa maimakon kashe kuɗaɗen jama’a kan motocin kamfen, gwamnati ta mayar da hankali kan samar da abinci, kiwon lafiya, ayyukan yi da inganta tsaro.

Karanta Wannan  Duk Duniya ba garin da nake so sama da Kano amma ba zan iya zama a Kano ba, Mai Wushirya yana can an kamashi saboda yawa Wada Khyss>>Inji G-Fresh Al-amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *