
Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa, dan kudu yake son a baiwa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV inda yace alkawari ne da ya kamata a ce an cikashi tsakanin mutanen Arewa da kudancin Najeriya.
Yace Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga Arewa yayi shekara 8 yana mulki hakanan ya kamata a bar kudu itama ta shakara 8 tana mulki kamin mulkin ya dawo Arewa.
Yace zai yi aiki tukuru dan ganin dan kudu ne aka tsayar takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 a jam’iyyar ADC.