
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya maka sanata Natasha Akpoti a kotu inda yace yana neman ta biyashi diyyar Naira Biliyan 200 saboda bata masa suna.
Akpabio yace Natasha ta mai karyar cewa ya nemi yin lalata da ita wanda hakan ya bata masa suna sosai an rika masa dariya da wulakanci.
Yace dan haka yana neman kotu ta tursasa Sanata Natasha Akpoti ta janye wannan zargi da take masa sannan ta goge duk wani abu me alaka da wannan zargi data wallafa a kafafen sada zumunta sannan kuma ta fito ta bashi hakuri.