
Kwamitin shugaban kasa dake kula da canja dokar Haraji ya bayyana shahararrun masu amfani da kafafen sada zumunta su 20 da za’a yi amfani dasu wajan tallata sabuwar dokar Haraji Gwamnatin.
An fitar da wadannan sunayene daga cikin guda sama da dubu 8 da aka mika sunayensu.
Financial Jennifer, Onlinebanker, Don Aza, Mary Efombruh, Baba Ogbon Awon Agba International, Perpetual Badejo, Personalfinancegirl, Tomi Akinwale, Emeka Ayogu, da Aderonke Avava.
Sauran sune Odunola Ewetola, Christiana Balogun, Mosbrief, Chidozie Chikwe, Zainulabideen Abdulazeez, Chinemerem Oguegbe, Oyagha Michael, Ayomide Ogunlade, Ayọ̀dèjì Fálétò, and Vera Korie.
Saidai a lurar da hutudole yayi dan Arewa ko daya a cikinsu.