
Gwamnan jihar Edo, Monday, Okpebholo yayi zargin cewa wani dan siyasa ne dake son cin zabe yake sawa ana garkuwa da mutane a Najeriya dan bata sunan Gwamnati.
Yace haka sukawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kuma sun samu nasara a wancan lokacin.
Saidai bai bayyana sunan dan siyasar da yake zargi ba.