
Hukumar sojojin saman Najeriya ta fitar da sanarwa game da jirgin saman C-130 da sojoji 11 dake kasar Burkina Faso.
Me magana da yawun hukumar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya fitar da sanarwar inda yace jirgin na kan hanya ne ya samu rangarda inda yayi saukar gaggawa a kasar ta Burkina Faso.
Yace wannan shine abinda dokar kasa da kasa ta tanada.
Yace jirgin bai taka kowace doka ba kuma suna nan kan bakansu na yiwa dokokin kasa da kasa biyayya.
Yace sojojin Najeriyar sun samu tarba me kyau a hannun hukumomin kasar Burkina Faso kuma da zaran komai ya daidaita, zasu ci gaba da tafiyarsu.