Monday, December 15
Shadow

Kalli Bidiyo: Shugaban Tshàgyèràn Dhàjì na jihar Zamfara ya fito yace ba za’a yi amfani da shi ba a batawa Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle suna ba, yace karyane ba Ministan ne ke daukar Nauyinsu ba

Shugaban masu garkuwa da mutane na jihar Zamfara, Bello Turji ya bayyana cewa, ba gaskiya bane ikirarin da wani me suna Musa yayi na cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ne ke daukar nauyinsu.

Bello Turji yace Shi kansa ya tsani Karamin Ministan dan a zamaninsa ne aka kashe mutu mutane sama da 70 dan haka tsakaninsa dashi saidai Allah.

Yace amma shi abinda yasa ya fito yayi magana shine ba zai yadda a yi amfani ko a hada kai dashi a batawa wani suna ba, yace au daga Allah ne babu wani me daukar nauyinsu.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *