
Tsohon Ministan Kwadago Chris Ngige ya nemi Beli bayan da Kotu tasa a daureshi a gidan yarin Kuje.
Yace yana fama da rashin lafiya, kamar yanda Lauyansa, Patrick Ikwueto ya bayyanawa me shari’a ta babbar kotun tarayya dake Gwarimpa a Abuja Justice Maryam Aliyu Hassan
Saidai Lauyan EFCC, Sylvanus Tahir, SAN yace kotun kada ta bayar da belinsa dan a baya ita EFCC ta sakeshi inda aka saka mai ranar da zai sake komawa dan ci gaba da bincike amma yaki komawa.
Yace tsohon Ministan ka iya tserewa idan aka bayar da belinsa.
Saidai Mai shari’a Maryam Aliyu Hassan tace a ci gaba da tsare Ngige a gidan yarin kuje har ranar 18 ga watan Disamba kamin ta yanke hukunci kan maganar Belin.