Ga kalaman Soyayya masu ratsa zuciya kamar haka:
Inibi ta
Ina son inta kallonki kullun.
Kin hadu fiye da misali.
Kina min kyau ko da babu kwalliyar hoda.
Kyanki na asali ne baya bukatar shafe-shafe.
Idan banji muryarki ba ji nake ranar babu armashi.
A duk lokacin da kike kusa dani, ji nake kamar shugaban kasa.
Bansan sanda bakina ke budewa ba da zarar na ganki.
Idanunki suna min kwarjini.
Naso ace dake na fara haduwa da ban kara kula kowace mace ba.
Bana iya kula sauran mata saboda soyayyarki ta min shamaki.
Dandanon soyayyarki ya fi na zuma dadi.
Da kin fito sauran mata ke kaucewa saboda kwarjini.
Kullun sai nazari nake dan samun kalmar da zan iya bayyana kalar soyayyar da nake miki amma na kasa.
Kin kasance min kamar jini da hanta.
Zuciya ta taki ce.
Ba na boye miki komai.
Zan iya baki komai dana mallaka.
Bana jin dadin komai idan ba tare dake ba.
Ina yawaita kiran sunanki a sujjada ta.
Na yadda in mutu akan soyayyarki.
Ban taba tunanin zan iya sake soyayya ba amma kin maidani ruwa tsundum.