
Tauraruwar Kafafen sada zumunta kuma ‘yar Kasuwa, Shafa Wali ta bayyana irin gwagwarmayar data yi wajan neman Masoyi na gari.
Ta bayyana hakane yayin da takewa Amarya da Ango huduba watau diyar Hafsat Idris da Angonta.
Tace ta yi soyayya a baya amma yaudararta ake. Tace dalili kenan ma da yasa ta hakura da soyayya.
Hakan yasa da yawa suka rika cewa ashe Budurwa ce, wasu sun rika kiranta da ta zo ta auri mahaifisu.