
Wadannan wakilan Gwamnatin Najeriya ne karkashin jagorancin ministan harkokin kasashen waje Yusuf Tuggar inda suka gana da shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore.
Sun mikawa Shugaba Traore da sakon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na nuna goyon bayan gwamnatinsa.
Sannan sun bayar da hakuri game da shiga kasar Burkina Faso da jirgin Najeriyar yayi.
Sun bayyana muhimmancin ci gaba da dangantaka tsakanin Najeriya da kasar Burkina Faso.