
Tauraron Mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa idan ya hadu da Naziru Sarkin Waka, zai tsaya ne ya ga zai kirashi da Sarkin Wakar Kasar Hausa ko kuwa?
Rarara dai an bashi sarautar Sarkin Wakar Qasar Hausa a Masarautar Daura wanda lamarin ya dauki hankula
Saidai a wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Hikima, Rarara yace, a baya idan yaga Naziru Sarkin Waka yana kiranshi da Sarki.
Yace amma yanzu idan suka hadu zai tsaya ne ya ga shin Nazirun zai kirashi da sunan Sarkin Wakar Qasar Hausa?