
Jami’in Hukumar ‘yansandan kasar Ghana, (ACP), Dennis Fiakpui yace takura a aure da saka damuwa babban laifine a kasar.
Yace a tsakanin ma’aurata, duk wanda ya hana dan uwansa ma’amalar aure, misali mace ta ki yadda da mijinta a gado, idan ya kai kara kuma kotu ta samu matar da laifi, zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari.
Yace hakanan itama idan macence mijinta baya kwanciyar aure da ita, zata iya kaishi kara a nema mata hakkinta.
Yace hakanan idan miji na dadewa a waje baya komawa gida da wuri ko kuma ya daina cin abincin matarsa, duka zata iya kaishi kara a bi mata hakkinta.