
Amurka ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa a fannin inganta kiwon lafiya lafiya mai ɗorewa na tsawon shekaru biyar da Najeriya, wadda ta kai kimanin dala biliyan 5.1, don inganta tsarin lafiyar ƙasa karkashin tsarin Amurka na samar da lafiya ga al’ummar duniya ta America First Global Health Strategy.
A karkashin wannan yarjejeniyar, Amurka za ta bayar da tallafi na dala biliyan 2.1, yayin da Najeriya za ta zuba dala biliyan 3.0 a kiwon lafiya a cikin shekaru biyar.
Saidai kasar Amurka tace a fi baiwa Kiristoci muhimmanci wajan bayar da kiwon lafiyar.
Wannan shi ne mafi girman haɗin gwiwa da kowace ƙasa ta yi tun lokacin da aka kaddamar da tsarin.
Yarjejeniyar za ta ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na Najeriya, ta ceci rayuka, kuma ta ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin Amurka da Najeriya.
Daga cikin tallafin, za a keɓe kimanin dala miliyan 200 domin tallafawa sama da cibiyoyin lafiya na addinin Kirista guda 900, don fadada damar samun kulawa ga cututtuka kamar HIV da TB, zazzabin cizon sauro, da kula da uwa da jariri.