
Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa Al’ummar Jihar sun taru inda aka sauke Qur’ani da kuma yiwa Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami Addu’ar Allah ya tsareshi daga sharrin EFCC.
Abubakar Malami dai yana tsare a hannun hukumar EFCC biyo bayan zargin da take masa na aikata ba daidai ba da kudaden kasa.
Tuni hukumar ta fara killace wasu kadarorinsa.