
Matashiya, Nabila Ibrahim Makama ta ki zuwa jami’a bayan kammala makarantar Sakandare inda ta gayawa iyayenta cewa, Qur’ani take son haddacewa.
Ta haddace Qur’ani, amma duk da haka tace a barta tana son rubutashi da ka kamin ta shiga jami’a, kuma ta yi hakan.
Bayan nan ne ta shiga jami’ar Maryam Abacha American University inda ta karanci kimiyyar bayanai.
Ta kammala da sakamako mafi kyawu a ajinsu, kuma jami’ar ta ce mata ta zabi duk makarantar da take so a Duniya zata dauki nauyin karatun ta zuwa can dan ta ci gaba da karatu.
