
Saidu Mohammed ya karbi shugabancin hukumar NMDPRA daga hannun Farouk Ahmed.
Farouk Ahmed dai shine shugaban Hukumar NMDPRA wanda Attajirin Najeriya, Aliko Dangote yawa tonon Silili yace ya biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta har dala Miliyan 7 a kasar Switzerland.
Dangote dai ya kai Farouk kara hukumar ICPC inda ya nemi a bincikeshi.
Daga karshe Farouk ya ajiye mukaminsa.
Hukumar NMDPRA tace wannan canjin shugabancin da aka samu zai tabbatar da ci gaba da kuma yin aiki yanda ya kamata.