
Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya bata yi kokari ba.
Yace Sojojin Najeriya na da kwarewa da makaman da zasu iya kai irin wannan hari.
Yace Yana kiran Gwamnati ta yanke hulda da Amurka sannan kuma idan taimakon yaki da ta’addanci take nema ta nema wajan kasashen Pakistan, Turkiyya ko China.
Yace dalili kuwa shine shugaban kasar Amirka, Donald Trump a wulakance yake kallon Najeriya