
Wani Balarabe da ya yiwa wani dan Najeriya gorin cewa a wajansu aka koyi addini, ya sha raddi daga wajan Gimba Kakanda.
Wani dan Najeriya ne ya nuna rashin jin dadi game da yanda kasar UAE ta taya Kiristoci murnar Kirsimeti.
Balaraben dan kasar ta UAE wanda ke amfanin da sunan Imam of Peace ya cewa dan Najeriyar ya kyalesu dan a wajansu aka koyi addinin Musulunci.
Saidai Gimba Kakanda yace masa Musulunci ya riga zuwa Afrika kamin yaje Madina ballantana ma kasarsa ta UAE.
Yace Musulunci ya je Ethiopia a wajan Sarki Najashi kamin ya je Madina.
Sannan kuma Allah yana kallon zuciya ne ba kabila ko kala ko kudi ba, wanda yafi jin tsoronsa shine wanda yafi kusanci dashi.