Wata kuri’ar jin ra’yin jama’a da aka gudanar a shafin sada zumunta na Twitter ta nuna cewa mafiya yawan mutane Muhammad Sanusi II suke so a matsayin sarkin Kano.
Mutane sama da Dubu uku(3000) ne suka bayyana ra’ayinsu akan wannan kuri’ar.
Dambarwar sarautar Kano ta ballene bayan da majalisar jihar ta tsige Aminu Ado Bayero ta kuma nada Muhammad Sanusi II a matsayin sabon sarki.
Aminu Ado Bayero yaki yadda da saukewar da aka masa inda ya koma Kano, ya kafa fada a gidan Nasarawa.
An samu wata kotu data hana tsige Aminu Ado Bayero wadda da wannan ne ya fake yake neman sake komawa kan kujerar sa.
Jami’an tsaron Kano sun nuna cewa suna goyon bayan Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kanone inda suka ce umarnin kotu zasu bi.