
Mawallafin Jaridar Sahara reporters kuma dan fafutuka, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, bai yadda da ikirarin shugaban kasar Amurka, Donald Trump ba na cewa, wai yana son ceton Kiristocin Najeriya ba.
Yace ta yaya Trump zai ce yana son ceton Kiristocin Najeriya amma ya hanasu shiga kasar Amurka?
Shugaba Donald Trump dai ya saka tsatstsauran mataki kan ‘yan Najeriya dake son shiga kasar Amurka ba tare da banbance musulmi ko Kirista ba.