
Wannan wani fasto ne Bayerabe da ya karbi Shahada Ranar Kirsimeti.
Yace yana cikin karanta Baibul ne sai ya je inda yaga cewa Jesus yayi Sallah irin ta musulmai.
Yace kuma yaga inda Jesus ya la’anci masu bauta ta hanyar rawa da waka, yace shine ya je ya nunawa faston dake gaba dashi.
Amma sai yace masa wai kuskurene aka yi.
Yace to shine yace waye yayi kuskuren, Jesus ne yayi kuskuren ko wanene?
Shine fa ya fara neman yanda zai musulunta inda yace bari yaje wajan malaman Hausawa yasan sune ba zasu karbi kudi da yawa ba.
Shine ya tambaya cewa nawa malaman Hausawa ke karba idan za’a shiga Musulunci? Aka ce masa kyautane shine ya musulunta.