
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, Harajin da Gwamnatin tarayya zata fara karba a hannun Talakawa Damfara ne.
Ya bayyana cewa, Har ‘yan majalisa sun bayyana cewa dokar da aka wallafa ba wadda suka amince da ita bace amma duk da haka gwamnatin ta yi gaban kanta tace sai ta karbi Haraji.
Yace Harajin zai kara Jefa ‘yan Najeriyar da yawa cikin Talauci ne.
Yace kuma ba da karbar Haraji ake ciyar da kasa gaba ba inda yace, ana ciyar da kasa gaba ne ta hanyar azurta ‘yan kasa ta hanyar baiwa kananan masana’antu damar fadada kasuwancinsu da sauran abubuwan karfafa tattalin arziki.