
Jam’iyyar APC a jihar Kwara ta zargi tsohon kakakin majalisar Dattijai, Bukola Saraki da cewa, yana Adawa a jihar Ta Kwara amma yana zagayawa ya rika ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Me magana da yawun jam’iyyar APC na jihar Kwara, Abdulwaheed Babatunde ne ya bayyana hakan, inda yace ya kamata Bukola Saraki ya fito ya gayawa mabiyansa bangaren da yake.
Yace a Kwara sai ya nuna shi dan PDP ne amma sai ya rika zuwa Abuja yana ganawa da shugaba Tinubu.