
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu dauka akan Abba idan ya koma jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa wadanda suka baiwa Abba shawarar komawa jam’iyyar APC, ya kamata su kuma bashi shawarar ajiye mukamin gwamna tunda a jam’iyyar NNPP ya sameshi.
Kwankwaso yace ji yake kamar a mafarki yake game da maganar komawar Abba jam’iyyar APC.
Ya kuma karyata rade-radin da ake cewa wai hada baki suka yi da Abba.