
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 7 dan inganta wutar Sola dake fadar shugaban kasar.
An ware wadannan kudade ne a kasafin kudin shekarar 2026.
A shekarar 2025 gwamnatin ta ware naira Biliyan 10 ne dan saka wutar Solar a fadar shugaban kasar.
Hakan na zuwane a yayin da lamarin wutar lantarki ke kara tabarbarewa a Najeriya.