
Wani bincike da aka wallafa a PLOS ONE wanda masana suka tabbatar da sahihancinsa yace maza da suka fito daga kauye sannan matalauta kuma masu fama da yunwa sun fi son mata masu manyan Nonuwa.
Hakanan a bangare guda kuma mazan da suke da dukiya da koshi sun fi son mata masu kana na da matsakaitan nonuwa.
Masana ilimin halayyar dan adam Viren Swami da Martin J. Tovée ne suka gudanar da wannan binciken.
Sannan sun gudanar da wannan bincikenne a kasashen Ingila da Malaysia.
Sun samu maza 266 daga kauyuka sannan mata lauta sannan kuma aka samu wasu mazan masu kudi.
Kowanne daga cikinay an nuna musu mataye masu manyan nonuwa da masu matsakaita da masu kananan nonuwa.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, maza da suka fito daga kauye sannan suke fama da Talauci sun fi son mata masu manyan nonuwa.
Hakanan maza da suke da rufin asiri sun fi son mace me matsakaicin nono zuwa manya.
Hakanan maza mawadata masu dukiya sun fi son mataye masu kananan nonuwa zuwa matsakaita.
Sannan sun kara yin wani binciken a kasar Ingila
Inda aka samu maza 124 aka ware wasu masu jin yunwa, wasu kuma suka ci abinci, sannan aka nuna musu mataye masu kanana da manyan nonuwa.
Masu jin yunwar sun zabi mata masu manyan nonuwa, inda kosassun maza suka zabi mata masu kananan nonuwa.