
Kasar Algeria ta shigar da Rafalin da ya hura wasan ta da Najeriya dan kasar Senegal me suna, Issa Sy kara.
Hakanan a yanzu tana son kara shigar da Rafalin kara a karo na biyu.
Hukumar kwallon kafa ta Algeria, FAF ce ta sanar da hakan inda suke zargin Rafalin da rashin Adalci.
Sun yi zargin cewa sun samu Penalty ya hana hakanan kuma bayan wasan ya gaisa da ‘yan wasan Najeriya amma bai gaisa da ‘yan wasan Algerian ba.
Hakanan kuma sun zargi cewa bayan an kammala wasan an co zarafinsu.
Wasan dai ya tashi Najeriya na cinsu 2-0.