
Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana’a ya bayyana cewa yana mika kokensa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima akan cewa ya yiwa APC wahala amma har yanzu ba’a bashi komai ba.
Ya bayyana cewa, dashi aka yi yakin neman zabe da komai amma ko sannu babu wanda yace masa.
Dan haka yace yasan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima mutum me me tausai shiyasa yake mika kokon bararsa a wajansa.
Ya bayyana hakane bayan da Mataimakin shugaban kasar ya baiwa abokin aikinsa, Adam A. Zango kyautar mota ta Naira Miliyan 80.