
Kotun koli ta tabbatar da daurin da akawa dan gidan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Aminu Sule Lamido.
A yau Juma’a ne kotun ta yi wannan hukunci inda tace daukaka kara da Aminu Sule Lamido yayi bashi bata bi ka’ida ba sannan ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da kotun Gwamnatin tarayya suka yi akansa.
A baya dai kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun Gwamnatin tarayya akan Aminu Sule Lamido.
An dai kama Aminu Sule Lamido ne da Dala $40,000 a filin jirgin sama wanda bai gayawa hukumomi cewa yana dauke da wannan kudaden ba.
A hukuncin da aka masa, an bukaci ya baiwa gwamnati kaso 25 cikin 100 na kudin nasa sannan an daureshi a gidan yari.