
A ranar Tunawa da ‘yan mazan jiya, Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya hadu da wani soja da ya rasa hannunsa a wajan aiki.
An gabatar da sojan a wajan gwamnan, inda gwamnan yace a yiwa sojan hannun Roba, inda yace a masa me kyau, har yana tambaya duka nawa yake?
Saidai wannan lamari ya jawo cece-kuce inda masu sharhi suka zargi gwamnan da rashin nuna tausai ga sojan musamman ganin cewa ya rasa hannun nasa ne wajan yiwa kasa Hidima.
Masu Sharhin na ganin cewa ba maganar kudi kawai bace, ya kamata gwamnan ya nuna alhini da halin da sojan ke ciki.