
Kungiyar goyon bayan Atiku Abubakar, me suna Atiku Haske Organization ta kori dan Atikun me suna Abba Atiku bayan da ya koma jam’iyyar APC.
Abba ya canjawa kungiyar suna zuwa ta goyon bayan Tinubu saidai shugaban kungiyar, Musa Bakari ya ce dan Atiku bai da hurumin canjawa kungiyar suna ko ya bayar da umarni ga mabiya kungiyar.
Yace sune suka kafa wannan kungiyar kuma shahadar yi mata rijista na hannunsu.
Yace dan haka sune masu gudanarwar kungiyar ba dan Atikun ba.
Dan haka yace sun koreshi daga kungiyar.