Tuesday, September 22
Shadow

Kungiyar Goyon bayan Atiku sun kori dan Atikun, watau Abba Atiku da ya koma jam’iyyar APC

Kungiyar goyon bayan Atiku Abubakar, me suna Atiku Haske Organization ta kori dan Atikun me suna Abba Atiku bayan da ya koma jam’iyyar APC.

Abba ya canjawa kungiyar suna zuwa ta goyon bayan Tinubu saidai shugaban kungiyar, Musa Bakari ya ce dan Atiku bai da hurumin canjawa kungiyar suna ko ya bayar da umarni ga mabiya kungiyar.

Yace sune suka kafa wannan kungiyar kuma shahadar yi mata rijista na hannunsu.

Yace dan haka sune masu gudanarwar kungiyar ba dan Atikun ba.

Dan haka yace sun koreshi daga kungiyar.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa game da yanda ake kirkiro Bidiyo na bogi na shugaban kasa dake nunashi a wani yanayi mara kyau domin ɓata masa suna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *