
Bidiyon matasan Yarbawa na rokon Shahararren me amfani da kafafen sadarwa na kasar Amurka, Ishowspeed da ya kawo Najeriya kudi ya dauki hankula.
An gansu suna bin motarsa suka mika masa hannu suna cewa ya basu kudi.
Lamarin ya jawo musu suka sosai inda da yawa ke cewa sun jawowa Najeriya abin kunya a Idon Duniya.
Wasu ‘yan Arewa sun rika cewa, kada wani ya kara zagin Arewa da cewa suna da Almajirai mabarata, tunda dai ta bayyana kowa yana roko.