
Wannan mutumin sunansa Ojo Eghosa Kingsley dan jihar Edo.
Kuma a watan Yuni na shekarar 2026 bankin First Bank sun tura masa Naira Biliyan 1.5 a matsayin kuskure.
Saidai maimakon ya mayarwa da bankin kudin, ya yi ta wadaka dasu inda ya rabasu zuwa asusun ajiyar bankin Mahaifiyarsa dana kanwarsa.
Da aka kamashi, EFCC ta kwace 1.1 Bidiyon daga hannunsa inda ya zama saura Naira Miliyan 272 wadda kotu ta ce ya biya bankin.
Saidai rahotanni sun bayyana cewa, ya ce ya zabi zama a gidan yari maimakon ya mayarwa da bankin kudin.