Wani magidanci dan kimanin shekaru 49 ya koka cewa, matarsa na barazanar kasheshi saboda ya kasa gamsar da ita a gado.
Lamarin ya farune a kasar Zambia inda mijin ya kai kara kotu.
Matar ta kuma yi barazanar fara yin lalata da wasu a waje idaan mijin ya kasa gamsar da ita.
Kafar Zambia Observer ta bayyana sunan mijin a da Dennis Sikanika inda tace matar kuma sunanta Faustina Chola.
Saidai mijin yace tun kamin su yi aure, ya gayawa matar tasa cewa, shi bashi da karfin mazakuta kuma ta yadda suka yi auren a haka.