
Wani Dan Jarida ya bayyana cewa, Babu Kwarewa game da yanda Madina Maishanu, ma’aikaciyar BBCHausa ta yi hira da jagoran Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya bayyana cewa, akwai ‘yan jarida da yawa na Duniya wanda suka yi hira da manyan mutane kuma sun rika dariya suna tattaunawa irin yanda ya kamata amma hakan bai sa sun sabawa dokar aikinsu ba.