
Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga Tauraron fina-finan Hausa, Dady Hikima wanda aka fi sani da Abale da abokan aikinsa suna tayashi murnar motar da akace Tinubu ya bashi kyauta.
A Bidiyon an ji yanawa shugaban kasa godiya yana kuma tabbatar da goyon bayansa gareshi.
Yayin da wasu suka yaba, wasu kuwa Allah wadai da hakan suka yi.