Monday, December 16
Shadow

Ƴansanda sun kori ƴandaba da mafarauta daga fadar Kano,ji dalili

Rundunar ƴansanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kori ƴandaba daga fadar sarkin Kano domin daƙile ayyukan dabanci a jihar.

Ƴandaba da mafarauta ne suka kasance suna gadin fadar, wadda Sarki Muhammadu Sanusi II ke zaune a cikin ta yanzu.

Wata majiyar jami’an tsaro ta sanar da PRNigeria cewa matakin ‘yan sandan ya biyo bayan rahotannin sirri da aka samu na kwararowar ƴandaba da ƴantauri wato mafarauta daga ƙananan hukumomi zuwa birnin.

Yanzu haka dai ƴansanda sun karbe iko da fadar ta Gidan Rumfa da ta Nasarawa, inda aka tura jami’ai zuwa wuraren da ke da rauni domin tabbatar da doka da oda.

Karanta Wannan  ‘Yansanda na bi gida-gida dan kama ‘yan daba dake shirin kai hari majalisar jihar Kano

Yayin da Muhammdu Sanusi II ke ci gaba da zama a Gidan Rumfa, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na zaune ne a fadar sarkin Kano da ke Nasarawa.

A kwanakin baya ne wata kotu da ke Kano ta ce duk wasu matakai da gwamnan jihar ya ɗauka bayan umarnin da ta bayar na kowa ya tsaya kan matsayinsa ya saɓa wa doka kuma haramtacce ne.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da taƙaddama kan sake naɗain na Muhammadu Sanusi II da kuma tuɓe rawanin Aminu Ado Bayero a kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *