Friday, March 13
Shadow

Kalli Bidiyon: Kirista Dalibar Kadpoly dake Kaduna ta koka da cewa, ana takura musu sai sun rufe jikinsu kamin su shiga makaranta saboda Musulmai na Azumi

Wata Kirista Dalibar Jami’ar Kaduna Polytechnic dake Kaduna ta koka da cewa ba’a musu Adalci inda tace sun saka kaya basu nuna komai na tsiraici ba amma an hanasu shiga makaranta.

Ta koka da cewa, Ana tilasta musu rufe jikine saboda musulmai dake Azumin watan Ramadana.

Tace wannan ba adalci bane.

Dalibar ta bayyana hakane a Bidiyon data yi a kofar makarantar bayan da aka hanasu shiga inda ta yi kira ga hukumomin makarantar su dauki mataki.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ban taba neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na yi rashin nasara ba>>Inji Atiku da aka tambayeshi ko yana ganin zai iya samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *