
Gwamnatin Kano za ta faɗi matsayarta kan hawan Sallah a yau
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta sanar da matsayarta kan hawan Sallah a jihar.
Mai magana da yawun Gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Gwamnatin Kano za ta fadi matsayar ta kan hawan sallah nan da yan awannan kadan ta bakin Kwamashinan Yada Labarai.
“A jira cikin lumana…”
Bayanin nasa na zuwa ne a yayin da ake takaddama kan wanda zai jagoranci hawan Sallah tsakanin Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero.