A yayin da ake ta cece-kuce kan cewa Idan mutum yayi Sallar Idi ba sai yayi ta Juma’a ba.
An samu karatun malamai dake tabbatar da hakan.
A jiya ne dai, Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa lallai ko da mutum yayi Sallar Idi, sai yayi Juma’a.
Malam yace idan za’a dauki daya a bar daya to mutum ya bar Idi yayi Juma’a.
Saidai Karatun malamai irin su Dr. Idris Dutsen Tanshi, da Sheikh Jafar Mahmoud Adam, da Sheikh Albani Zaria duk sun tafi akan cewa, idan mutum yayi Idi, ba lallai sai yayi Juma’a ko Azahar ba.