Wednesday, March 25
Shadow

Duk da saukar farashin mai a kasuwannin Duniya, ‘Yan kasuwar man fetur na Najeriya sun ki rage farashi

Rahotanni na cewa a kasuwar Duniya, Farashin danyen man fetur ya fadi zuwa dala $100 daga dala $130.

Saidai duk da hakan, ‘yan kasuwar man fetur din na Najeriya suna ci gaba da sayar da man da tsada a farashin Naira 1,300 akan kowace lita.

Saukar farashin a kasuwar Duniya ya farune a yayin da ake tsammanin tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran zata haifar da da me ido.

Saidai duk da wannan, gidajen man fetur a Najeriya ciki hadda na gwamnati, NNPCL suna sayar da man akan farashi sama da Naira 1,300 a wasu gidajen man ma har sama da hakan.

Hauhawar farashin man fetur din a Najeriya yasa an samu hauhawar wasu kayan masarufi dama ababen hawa.

Karanta Wannan  Mutane 30 Sun Mutu An Kwantar Da Wasu Gommai a Asibiti Bayan Sun Sha Burkutu a India

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *