Ko kunsan cewa, zaku iya hada man kwakwa a gida, ana amfani da man kwakwa sosai a sassa daban-daban na Duniya.
Matakan hada man Kwakwa:
A fasa kwakwar.
A cire bawon kwawar ya zamana sai kwakwar ita kadai.
A yi amfani da greater ko wuka ko wani abin yanka a yi gutsi-gutsi da kwakwar, ana iya markado ta idan ana neman sauki.
Sai kuma ayi ko a hada madarar kwakwa, ta hanyar tace kwakwar bayan an markadota. Idan ana da blender ana iya zuba kwakwar da aka yanka kanana-kanana a zuba ruwa dan kadan a yi blinding, sai a tace da rariya.
Bayan an samar da madarar kwakwar sai a zubata a tukunya a tafawa na tsawon awa daya ko biyu, man kwakwar zai taso sama.
Idan ya tafasa sosai, zaki ga madarar ta yi duhu kuma man kwakwar ya fita daban daga jikin madarar.
Sai a tace a fitar da madarar daban man daban.
Ana iya ajiye man a firjin. Ana amfani dashi wajan gyaran fata, gyaran fuska, gyaran gashi da kuma cin abinci ko soya kayan fulawa.
[…] Ana iya amfani da man shafawa mai laushi bayan wanke fuskarka, misali ana iya amfani da man kwakwa. […]
[…] Man kwakwa yana da fa’idodi masu yawa ga gashi. […]
[…] Kwakwa: Bayan Man zaitun, ana kuma amfani da Man Kwakwa wanda ba’a gaurashi da komai ba wajan gyaran […]