
Matashiya ‘yar Arewa dake aikin Fenti me suna Amira ta dauki hankula bayan da aka ganta tana aikin Fentin.
Bayan da Bidiyon ta ya bayyana tana Fenti, wasu sun rika kiran cewa ya kamata tana saka hijabi.

Saidai a martaninta tace lallai tana saka Hijabi daga gida, amma idan taje wajan aiki ne take cirewa saboda ba zai yiyu ta yi aiki da Hijabin ba.